(ABNA24.com) Yau Lahadi, kasashen da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran, ke taro, a birnin Vienna, na kasar Austiriya, da manufar ceto yarjejeniyar, dake tangal-tangal bayan ficewar Amurka, da kuma yadda Iran ta fara daina aiki da wasu daga cikin sharudda da aka kayyade mata a cikin yarjejeniyar.
Yarjejeniyar wacce aka cimma a shekarar 2015, tsakanin manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka, Birtaniya, Rasha, China, Faransa da kuma Jamus, ta tanadi dage wa Iran jerin takunkuman kasa da kasa da aka kakaba mata kan shirinta na nukiliya, saidai bayan kama mulki shugaba Trump yayi watsi da yarjejeniyar ta hanyar janye Amurka daga cikinta a watan Maris na shekara 2018, tare da kakaba wa Iran takunkumai.
Kusan shekara guda kenan da Iran, take bayan sauran kasashen da suka rage a cikin yarjejeniyar dasu samar mata da mafita, sakamakon jerin takunkuman da Amurka ta kakaba mata musamman kan harkokin bankuna da man fetur.
Sakamakon rashin tabuka komai ne daga sauran kasashen da suka rage a yarjejeniyar, Iran ta sanar da fara shirinta na daina aiki da wasu daga cikin sharudda da yarjejeniyar ta kunsa, ciki har da batun tatse sinadarin uranium sabanin yadda aka kayyade mata.
A taron da zasu gudanar yau Lahadi, kasashen da suka rage a yarjejeniyar, na son Iran ta mutunta yarjejeiyar da aka cimma da ita dalla-dalla.
/129
29 Yuli 2019 - 03:58
Lambar labari: 965486
Yau Lahadi, kasashen da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran, ke taro, a birnin Vienna, na kasar Austiriya, da manufar ceto yarjejeniyar, dake tangal-tangal bayan ficewar Amurka, da kuma yadda Iran ta fara daina aiki da wasu daga cikin sharudda da aka kayyade mata a cikin yarjejeniyar.